Daya daga cikin Sanatocin jihar Kaduna ya caccaki El-Rufa’i, ya kira shi takadari
Hotunan yadda Buhari ya karrama Moshood Abiola Shugaban ya karrama marigayi Moshood Abiola ne da babbar lambar yabon kasar a Abuja a ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.
Shugaba Buhari ya mika wa dan marigayin Kola Abiola lambar GCFR a madadin mahaifinsa
Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar a Abuja a ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993
Marigayi Abiola ya rasu ne a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1998
Dan marigayin Kola shi ne ya karbi lambar yabon ta GCFR a madadin mahaifinsa yayin taron, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa
Lokacin da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Buhari ya nemi gafarar iyalan marigayin da kuma sauran mutanen da suka rasa rayukansu a fafutikar June 12
Cikin wadanda suka samu halartar taron har da jigo a jam'iyyar APC mai mulki Alhaji Bola Ahmed Tinubu da sauran manyan jami'an gwamnati
Har ila yau Farfesa Wole Soyinka da kuma Ministan Ayyuka da Lantarki da kuma Gidaje Babatunde Fashola sun halarci taron
Taron da kuma matakin karrama mutumin da ake ganin shi ya lashe zaben na 1993, ya raba kawunan 'yan kasar tsakanin masu murna da kuma masu adawa
Baba Gana Kingibe da marigayi Gani Fawehinmi sun samu lambar GCON ne
Hakazalika an gudanar da taron tunawa da zaben 12 ga watan Yunin a wadansu jihohin kasar ciki har da Legas